Ishaya 27:13 - Sabon Rai Don Kowa 202013 Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki13 A wannan rana za a busa ƙaho don a kirawo Isra'ilawan da suke zaman baƙunci a Assuriya da Masar. Za su zo su yi wa Ubangiji sujada a Urushalima a tsattsarkan dutsensa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”