ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba.
Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”
Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne.
Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.
yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi.
Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.