“A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar.
“Zan hallaka mutane da dabbobi; zan kuma hallaka tsuntsayen sama da kifayen teku, da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.” “Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,” in ji Ubangiji.
Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da mugayen siffofi ko kuma da wani daga laifofinsu ba, gama zan cece su daga dukan zunubinsu na ridda, zan kuma tsarkake su. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu.
A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub, wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa. Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu, har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare da za a bari a tsaye.
Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin tare da ƙungiyar dawakai. Ya kuma mayar da amsa, ‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi! Dukan siffofin allolinta kwance a ragargaje a ƙasa!’ ”
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.
Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.”
Duk inda kuke zama, garuruwa za su zama kango, za a kuma ragargaza masujadai, saboda bagadanku su rurrushe su zama kango, a kuma farfasa gumakanku su lalace, za a rurrushe bagadan ƙone turarenku, a kuma shafe dukan abin da kuka yi.