In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.
Za su ratsa cikin tekun wahala; zan kwantar da raƙuman teku dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe. Za a ƙasƙantar da Assuriya, sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.
Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa? Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa? Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka? Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne? Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku, na mai da koguna hamada; kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa suka kuma mutu saboda ƙishi.