Ishaya 17:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Ba za su dubi bagade ba, waɗanda suke aikin hannuwansu, ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Ba za su ƙara dogara ga bagaden da suka yi da hannuwansu ba, ko kuwa su dogara ga ayyukan hannuwansu, ko keɓaɓɓun wuraren da suke wa gumaka sujada, ko bagadai don ƙona turare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa.