Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 17:6 - Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Duk da haka waɗansu kala za su ragu, sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun, aka bar ’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai ’ya’ya,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

6 Isra'ila kuma za ta zama kamar itacen zaitun wanda aka karkaɗe 'ya'yansa, aka bar biyu ko uku kawai a ƙwanƙolin itacen, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassansa. Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 17:6
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Haka zai zama a duniya da kuma a cikin al’ummai, kamar sa’ad da akan karkaɗe itacen zaitun, ko kuma kamar sa’ad da ake barin kala bayan an girbe inabi.


Ubangiji zai watsar da ku a cikin mutane, ɗan kaɗan ne kaɗai za su ragu a cikin al’umman da Ubangiji zai kai ku.


Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto.


“In ɓarayi suka zo miki, in kuma ’yan fashi suka shigo gidan da dare, kash, bala’i zai jira ki ba abin da suke so ne kawai za su sata ba? In kuma masu tsinka ’ya’yan inabi suka zo miki, ba sukan bar ’ya’yan inabi kaɗan ba?


Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba?


Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.


Tawa ta ƙare! Ina kama da wanda yake tattara ’ya’yan itatuwa a lokacin kalar ’ya’yan inabi; babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci, babu kuma ’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.


Ba zan ƙara kawar da fuskata daga gare su, gama zan zuba Ruhuna a kan gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”


A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya.


Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku, raguwa ce kurum za tă komo. A ƙaddara hallaka, mai mamayewa da mai adalci.


Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana raguwar masu rai ba, da mun zama kamar Sodom, da mun zama kamar Gomorra.


Duk da haka zan bar mutane dubu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su rusuna da gwiwansu wa Ba’al ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”


Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dukan ƙasar za tă zama kufai, ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ