Ishaya 15:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne, An lalatar da Ar a Mowab, an hallaka ta da dare! An lalatar da Kir a Mowab, an hallaka ta da dare! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Wannan shi ne jawabi a kan Mowab. Biranen Ar da Kir, an hallaka su dare ɗaya, ƙasar ta yi tsit, ba kowa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka ragargaza garuruwa, kowane mutum kuwa ya jefa dutse a kowane gona mai kyau har sai da aka rufe gonakin gaba ɗaya. Suka tattoshe duk maɓulɓulan ruwa, suka kuma sare duk itace mai kyau. Kir Hareset ne kaɗai aka bari tare da duwatsunsa yadda suke, amma mutanen da suke da majajjawa suka yi wa birnin zobe, suka kai masa hari shi ma.