Ishaya 14:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”