Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Abin da Allah ya faɗa game da Masar, Duba, Ubangiji yana a kan girgije a sukwane yana kuwa zuwa Masar. Gumakan Masar sun firgita a gabansa, zukatan Masarawa sun karai.
Mutanensu, suka rasa ƙarfi, sun firgita suka kuma sha kunya. Suka zama kamar tsire-tsire a gona, kamar tsire-tsiren ta suka tohu, kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi, wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.
Sojojin Babilon sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata. An sa wa wuraren zamanta wuta, an karya ƙyamaren ƙofofin garinta.