15 Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
15 Duk wanda aka kama za a soke shi ya mutu.
Ku kashe dukan ’yan bijimanta bari su gangara zuwa mayanka! Kaitonsu! Gama ranansu ta zo, lokaci ya yi da za a hukunta su.
Ubangiji ya buɗe taskar makamansa ya fitar da makaman fushinsa, gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yi a ƙasar Babiloniyawa.
Sun gudu daga takobi, daga takobin da aka janye, daga bakan da aka tanƙware da kuma daga zafin yaƙi.
da kai ne na ragargaza miji da mata, da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi, da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa,