Ishaya 10:20 - Sabon Rai Don Kowa 202020 A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki20 Lokaci zai yi sa'ad da jama'ar Isra'ila da suka ragu ba za su ƙara dogara ga al'ummar da ta kusa hallaka su ba. Hakika za su dogara ga Ubangiji Allah, Mai Tsarki na Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”