Ishaya 1:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 Ya ce, “Kuna tsammani ina jin daɗin dukan hadayun nan da kuke ta miƙa mini? Tumakin da kuke miƙawa hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da na awaki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;