Irmiya 8:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Za a kunyatar da masu hikima; za su yi fargaba a kuma kama su. Da yake sun ƙi maganar Ubangiji, wace irin hikima kuka ce kuke da ita? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Za a kunyatar da masu hikima. Za su tsorata, za a kuma tafi da su. Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji. Wace hikima suke da ita? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.