Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.
Game da annabawa kuwa, Zuciyata ta karai; dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa. Na zama kamar wanda ya bugu, kamar mutumin da ruwan inabi ya sha kansa, saboda Ubangiji da kuma maganarsa mai tsarki.
Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi.