Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa, mun kuma yi yarjejjeniya da kabari. Sa’ad da zafi ya ratsa, ba zai taɓa mu ba, gama mun mai da ƙarya mafakarmu ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.”
Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.
Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu gonakinsu kuma ga waɗansu da suka ci da yaƙi. Tun daga ƙarami har zuwa babba, kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba; har da annabawa da firistoci ma, kowannensu yana ƙarya.
Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.”
Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.
Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.
Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya.