“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan? Kana ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu don kada mu warke? Mun sa zuciya ga salama babu abin alherin da ya zo, mun sa rai ga lokacin warkarwa amma sai ga razana.
Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa.