Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda, nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari, kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi, tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina! Na suma; an ba da raina ga masu kisana.”
Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ke Diyar Urushalima? Da me zan misalta ki, yadda zan iya yi miki ta’aziyya, Ke Budurwa Diyar Sihiyona? Ciwonki yana da zurfi kamar teku. Wane ne zai iya warkar da ke?
Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona da gizagizan fushi! Ya jefar da darajar Isra’ila daga sama zuwa ƙasa; bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba a ranar fushinsa.
Mace mafi hankali da kuma kirki a cikinku, kai, mafi hankali da kirki da ba ta ma karambanin taɓa ƙasa da tafin ƙafarta, za tă hana wa mijinta da take ƙauna, da kuma ɗanta, ko ’yarta abinci.