Sojojin Babilon sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata. An sa wa wuraren zamanta wuta, an karya ƙyamaren ƙofofin garinta.
Tabbas suna kama da bunnu; wuta za tă cinye su ƙaf. Ba za su ma iya ceton kansu daga ikon wutar ba. Ba wutar da wani zai ji ɗumi; ba wutar da za a zauna kusa da ita.
Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce, “’Yar Babilon kamar daɓen masussuka a lokacin da ake sussuka, ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.