Irmiya 50:29 - Sabon Rai Don Kowa 202029 “Ku kira ’yan baka a kan Babilon, dukan waɗanda suke jan baka. Ku yi sansani kewaye da ita duka; kada ku bar wani ya tsira. Ku sāka mata don ayyukanta; ku yi mata yadda ta yi. Gama ta tayar wa Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki29 “Ku kirawo 'yan baka, dukan waɗanda sukan ja baka, su faɗa wa Babila. Ku kafa sansani kewaye da ita, kada ku bar kowa ya tsira. Ku sāka mata bisa ga dukan ayyukanta, gama ta raina Ubangiji Mai Tsarki na Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.