Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 50:25 - Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Ubangiji ya buɗe taskar makamansa ya fitar da makaman fushinsa, gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yi a ƙasar Babiloniyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

25 Ubangiji ya buɗe taskar makamansa, Ya fito da makaman hasalarsa, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana da aikin da zai yi a ƙasar Kaldiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 50:25
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama Ubangiji zai rushe Babilon, zai sa ta ƙame bakinta na alfarma. Sojoji za su yi ta kutsawa kamar raƙuman ruwa; suna tā da muryoyinsu.


“Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse.


Ku yi kuwwa a kanta a kowane gefe! Ta miƙa wuya, hasumiyarta ta fāɗi, katangarta sun rushe. Da yake wannan sakayya ce ta Ubangiji, ku ɗauki fansa a kanta; yi mata yadda ta yi wa waɗansu.


Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.


Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?


“Kai ne kulkin yaƙina, kayan yaƙina, da kai ne na ragargaza ƙasashe, da kai ne na hallaka mulkoki,


Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki; bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka.


Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi; ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja.


Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ