A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tattambaya a cikin al’ummai. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu mafi banƙyama.