Irmiya 5:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki15 “Ya ku mutanen Isra'ila, ga shi, ina kawo muku Wata al'umma daga nesa,” in ji Ubangiji, “Al'umma ce mai ƙarfin hali ta tun zamanin dā. Al'umma wadda ba ku san harshenta ba, Ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma.