Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu.
Zan ragargaza Elam a gaban maƙiyansu, a gaban waɗanda suke neman ransu; zan kawo masifa a kansu, da zafin fushina,” in ji Ubangiji. “Zan runtume su da takobi sai na kawo ƙarshensu.