Zai sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi.
Mai ɗaga kai za tă yi tuntuɓe ta kuma fāɗi kuma ba wanda zai taimake ta tă tashi; zan hura wuta a garuruwanta da za tă cinye duk waɗanda suke kewaye da ita.”