43 Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen Mowab,” in ji Ubangiji.
43 Tsoro, da rami, da tarko suna jiranku, Ya mazaunan Mowab, Ni Ubangiji na faɗa.
Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”
A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu.
Zan kawo razana a kanki daga waɗanda suke kewaye da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Za a kore kowannenku, babu wani da zai tattara masu gudun hijira.
Na sa miki tarko, Babilon, kika kuwa kamu kafin ki sani; aka same ki aka kuma kama ki domin kin tayar wa Ubangiji.