Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab; mutanenta sun gudu har zuwa Zowar, har zuwa Eglat Shelishiya. Sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka; a kan hanyar zuwa Horonayim suna makoki saboda hallakawarsu.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa
Dibon ya haura zuwa haikalinta, zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka; Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba. An aske kowane kai an kuma yanke kowane gemu.