“Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai.
Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.
Dibon ya haura zuwa haikalinta, zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka; Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba. An aske kowane kai an kuma yanke kowane gemu.