Gama ya ce, “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.
“ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Daga Migdol zuwa Aswan za su mutu ta wurin takobi a cikinta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Tsoron da ka sa ake ji da kuma girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, kai da kake zama a kogon dutse, kai da kake kan tudu. Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa, daga can zan sauko da kai ƙasa,” in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa,
Na kuma ga wani abu a duniya. Ba kullum maguji ne yake nasara a tsere ba, ba kullum jarumi ne yake yin nasara ba, ba kullum mai hikima ne da abinci ba ba kullum mai basira ne yake da wadata ba ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba; amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.