Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 47:3 - Sabon Rai Don Kowa 2020

3 da jin motsin takawar kofatan dawakai, da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba da motsin ƙafafunsu. Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba; hannuwansu za su yi laƙwas.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

3 Da jin takawar kofatan dawakai, Da amon karusai da ƙafafun karusai, Ubanni ba su juya, su dubi 'ya'yansu ba, Domin hannuwansu sun yi laƙwas,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 47:3
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Daga Dan ana jin tirjin dawakan abokin gāba; da jin haniniyar ingarmunsu dukan ƙasar ta girgiza. Sun zo su cinye ƙasar da kome da yake cikinta, birni da dukan mazaunanta.


Sa’an nan kofatan dawakai suka ƙwaƙula, suna sukuwa, haka dawakansa masu ƙarfi suke tafiya.


Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, suna kai da kawowa a dandali. Suna walƙiya kamar tocila suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.


Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai! Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi! Ku yi ta fitowa, ya jarumawa, mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi, mutanen Lidiya, masu iya jan baka.


Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi.


Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne marasa tausayi. Amonsu ya yi kamar rurin teku yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa kamar mutane a dāgār yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Babilon.


Za su yi gāba da ke da kayan yaƙi, kekunan yaƙi da kekunan doki da mutane masu yawa; za su ja dāgā a kanki a kowane gefe da garkuwoyi manya da ƙanana da kuma hulunan kwano. Zan miƙa ke gare su don hukunci, za su kuma hukunta ki bisa ga shari’arsu.


Ninebe tana kama da tafki, wanda ruwanta yana yoyo. Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” amma ba wanda ya waiga.


Kibiyoyinsu masu tsini ne, an ɗaura dukan bakkunansu; kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ