Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa
“Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba, kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba? Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu; za a dama ta sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar.
Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara.
Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.”
Wace ce wannan da take haurawa daga hamada tana dogara a kan ƙaunataccenta? A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, a wurin da aka haife ki, wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa. “ ‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai; kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna kana ɓullowa cikin rafuffukanka, kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka.
’Ya’yansa maza za su yi shirin yaƙi za su kuma tattara babbar rundunar sojoji, waɗanda za su yi ta mamayewa kamar rigyawar da ba iya tarewa, kuma za su kai yaƙin har kagararsa.