Irmiya 44:23 - Sabon Rai Don Kowa 202023 Domin kun ƙone turare kuka kuma yi wa Ubangiji zunubi ba ku kuma yi masa biyayya ko ku kiyaye dokarsa ko ƙa’idodinsa ko farillansa ba, wannan masifa ta aukar muku, yadda yanzu kuka gani.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki23 Saboda kun ƙona turare, kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, ba ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da sharuɗansa ba, shi ya sa wannan masifa ta auko muku a yau.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.