Irmiya 44:22 - Sabon Rai Don Kowa 202022 Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki22 Ubangiji ba zai yarda da mugayen ayyukanku ba, da ƙazantarku da kuka aikata, don haka ƙasarku a yau ta zama kufai ba mai zama a cikinta. Ta zama abin ƙyama da la'ana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.