Irmiya 44:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki17 Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku!