“Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes.
“Ka yi shelar wannan a Masar, ka kuma furta shi a Migdol; ka yi shelarsa kuma a Memfis da Tafanes. ‘Ku ɗauki matsayinku ku kuma shirya, gama takobi na cin waɗanda suke kewaye da ku.’
Duhu ne zai zama rana a Tafanes sa’ad da na karye ikon Masar; a can ƙarfin da take fariya zai ƙare. Za a rufe ta da gizagizai ƙauyukanta kuma za su tafi bauta.