Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, na kafa dutse a Sihiyona, dutsen da aka gwada, dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe; wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.
Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba.
Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!
Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon.