Irmiya 41:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 Sai Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka bi da dukan waɗanda suka tsira daga Mizfa waɗanda ya karɓe daga Ishmayel ɗan Netaniya bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato, sojoji, mata, yara da fadawan da ya kawo daga Gibeyon အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16 Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama'a, waɗanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da dukan hafsoshin soja tare da mutanensu suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya a matsayin gwamna, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Mutanen da suka zo su ne, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan ɗan Kareya, Serahiya ɗan Tanhumet mutumin Netofa, Ya’azaniya ɗan mutumin Ma’aka, tare da mutanensu.