“Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin! Ku gudu daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa! Ku ba da alama a Bet-Hakkerem! Gama masifa tana zuwa daga arewa, mummunar hallaka ce kuwa.
Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi.
Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.
Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima.
Annabin Irmiya ya tsara waƙoƙin makoki domin Yosiya, wanda har wa yau mawaƙa maza da mata suke rera game da Yosiya. Suka sa waɗannan su zama al’ada a Isra’ila, suna kuma a rubuce cikin Littafin Makoki.
“Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.”