Irmiya 4:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 “In za ka komo, ya Isra’ila, ka komo gare ni,” in ji Ubangiji. “In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana ba ka ƙara karkace ba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji ya ce, “Ya mutanen Isra'ila, idan za ku juyo ku komo wurina, Idan kuka kawar da abubuwan banƙyama daga gabana, Kuka kuma bar yin shakka, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji.