Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 39:16 - Sabon Rai Don Kowa 2020

16 “Tafi ka faɗa wa Ebed-Melek mutumin Kush, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ina gab da cika maganata a kan wannan birni ta wurin masifa, ba wadata ba. A lokacin za tă cika a idanunka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

16 “Ka tafi ka faɗa wa Ebedmelek mutumin Habasha, cewa Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Zan sa masifa, ba alheri ba, ta auko wa wannan birni. Wannan kuwa zai faru a kan idanunka a wannan rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 39:16
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.


Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku? “Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ ”


Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.


Zan hukunta shi da kuma ’ya’yansa da masu hidimarsa saboda muguntarsu; zan kawo kowace masifar da na furta a kansu da kuma waɗanda suke zama a Urushalima da na Yahuda, domin sun ƙi su saurara.’ ”


“Saboda haka, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa Yahuda da kuma kowane mutumin da yake zama a Urushalima kowace masifar da na ambata a kansu. Na yi musu magana, amma ba su saurara ba; na kira su, amma ba su amsa ba.’ ”


Zan yi umarni, in ji Ubangiji, zan kuma komo da su wannan birni. Za su kuwa yi yaƙi da ita, su ƙwace ta su kuma ƙone ta. Zan kuma mai da garuruwan Yahuda kufai don kada wani ya zauna a can.”


(To, fa, Uriya ɗan Shemahiya daga Kiriyat Yeyarim wani mutum ne wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji; ya yi annabci irin abu ɗaya gāba da wannan birni da wannan ƙasa yadda Irmiya ya yi.


“Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’


Ku tabbata dai, cewa in kuka kashe ni, za ku jawo wa kanku alhakin jini marar laifi a kanku da a kan birnin nan da kuma a kan masu zama a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”


Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci.


Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.


Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.


Gama ina lura da su don lahani, ba alheri ba; mutanen Yahuda da suke a Masar za su hallaka ta wurin takobi da yunwa sai dukansu sun hallaka.


Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta, a can zan umarci takobi yă kashe su. “Zan sa musu ido don mugunta ba don alheri ba.”


Yanzu kuma Ubangiji ya cika shi; ya yi kamar yadda ya faɗa. Dukan wannan ya faru domin kun yi zunubi ga Ubangiji ba ku kuwa yi masa biyayya ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ