Irmiya 39:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 suka aika aka kawo Irmiya daga gidan waƙafi, suka ba da Irmiya amana ga Gedaliya, ɗan Ahikam ɗan Shafan, don ya kai shi gida. Da haka Irmiya ya zauna tare da mutane. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi.