Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 38:22 - Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Za a fitar da dukan matan da suka ragu a fadan sarkin Yahuda wa hafsoshin sarkin Babilon. Waɗannan mata za su ce maka, “ ‘Sun ruɗe ka suka kuma rinjaye ka, waɗannan abokanka. Ƙafafunka sun nutse a cikin laka; abokanka sun yashe ka.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

22 Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa, “ ‘Aminanka sun ruɗe ka, Sun rinjaye ka. Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutse cikin laka, Sai suka rabu da kai.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 38:22
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.


Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta.


Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya.


Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka.


“Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini.


Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa.


Sarki Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawan da suka tafi wurin Babiloniyawa, gama Babiloniyawa mai yiwuwa su ba da ni gare su su kuma wulaƙanta ni.”


Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa, “Razana ta kowace fuska! Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!” Dukan abokaina suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa, “Mai yiwuwa a ruɗe shi; sai mu yi nasara a kansa mu ɗau fansa a kansa.”


Za a ba da gidajensu ga waɗansu, tare da gonakinsu da matansu, sa’ad da na miƙa hannuna gāba da waɗanda suke zama a ƙasar,” in ji Ubangiji.


Amma waɗanda suka dogara ga gumaka, waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’ za a mai da su baya da kunya.


Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye.


Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.


Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.


Sojojin da ta yi hayarsu a cikinta suna kamar ’yan maruƙa masu kitse. Su ma za su juya su kuma gudu gaba ɗaya, ba za su iya tsayawa ba, gama ranar masifa tana zuwa a kansu, lokacin da za su sha hukunci.


Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, an ci jarumawansu. Suna gudu da sauri ba waiwayawa, akwai razana a kowane gefe,” in ji Ubangiji.


Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu gonakinsu kuma ga waɗansu da suka ci da yaƙi. Tun daga ƙarami har zuwa babba, kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba; har da annabawa da firistoci ma, kowannensu yana ƙarya.


Me za ku ce sa’ad da Ubangiji ya naɗa muku waɗanda ku kanku kuka koya musu a matsayi abokai na musamman? Ashe, azaba ba za tă auko muku kamar na mace mai naƙuda ba?


Amma in ka ƙi miƙa wuya, ga abin da Ubangiji ya bayyana mini.


Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani,


Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku.


‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ