Irmiya 34:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’