Irmiya 33:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera, “Yana da kyau; ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije,