Irmiya 32:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kuɓuta daga hannuwan Babiloniyawa ba amma tabbatacce za a ba da shi ga sarkin Babilon, zai kuwa yi masa magana fuska da fuska ya kuma gan shi da idanunsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’