Irmiya 32:32 - Sabon Rai Don Kowa 202032 Mutanen Isra’ila da na Yahuda sun tsokane ni ta wurin dukan muguntar da suka aikata su, sarakunansu da fadawansu, firistocinsu da annabawa, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki32 Wannan kuwa saboda muguntar jama'ar Isra'ila ce da ta Yahuza, wadda suka yi don su tsokane ni in yi fushi, su da sarakunansu, da shugabanninsu, da firistocinsu, da annabawansu, da mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa.