Irmiya 32:29 - Sabon Rai Don Kowa 202029 Babiloniyawan da suke yaƙi da wannan birni za su zo ciki su cinna masa wuta; tare da gidaje inda mutane suka tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙona turare a rufin ɗakuna wa Ba’al suka zub da hadayun sha wa waɗansu alloli. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki29 Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba'al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku!