Irmiya 30:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Gama kwanaki suna zuwa sa'ad da zan komo da mutanena, wato Isra'ila da Yahuza. Zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu, za su kuwa mallake ta,’ ni Ubangiji na faɗa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.