Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 30:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 ’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā jama’arsu kuma za su kahu a gabana; zan hukunta duk wanda ya zalunce su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

20 'Ya'yansu za su zama kamar dā, Jama'arsu kuma za su kahu a gabana, Zan hukunta dukan waɗanda suka zalunce su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 30:20
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan ba su zuciya ɗaya da aiki ɗaya, don kullum su ji tsorona domin amfaninsu da kuma amfanin ’ya’yansu a bayansu.


Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji, nunan fari na girbinsa; dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi, masifa kuwa ta same su,’ ” in ji Ubangiji.


Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Allahnki, wanda ya kāre mutanensa, “Duba, na ƙwace daga hannunki kwaf da ya sa ki tangaɗi; daga wannan kwaf, kwaf na fushina, ba za ki ƙara sha ba.


Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu; za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi. Sa’an nan dukan mutane za su sani cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.”


’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.”


Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji,


“ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.


Da adalci za a kafa ke. Zalunci zai yi nesa da ke; ba za ki kasance da wani abin da za ki ji tsoro ba. Za a kawar da duk wani abin banrazana; ba zai yi kusa da ke ba.


Titunan birnin za su cika da samari da ’yan mata suna wasa.”


Zan ba da alama in kuma tattara su. Ba shakka zan fanshe su; za su yi yawa kamar yadda suke a dā.


Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā


“Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ