Irmiya 30:18 - Sabon Rai Don Kowa 202018 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki18 Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan komar wa alfarwar Yakubu arzikinta, Zan kuma nuna wa wuraren zamansa jinƙai, Za a sāke gina birnin a kufansa, Fādar kuma za ta kasance a inda take a dā. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.