Irmiya 3:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 “Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 “Ku komo, ya ku mutane marasa aminci, Gama ni ne Ubangijinku. Zan ɗauki mutum guda daga kowane gari, In ɗauki mutum biyu daga kowane iyali, Zan komo da su zuwa Dutsen Sihiyona. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.